Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno, ya koka kan yadda ’yan Boko Haram suka fara ɓuya a sansanonin ’yan gudun hijira da ke jihar.
Gwamnan ya ce suna aikata munanan laifuka da ke ƙara taɓarɓarewar tsaro a jihar.
- Mahara sun ƙona Sakatariyar Karamar Hukuma bayan janyewar ’yan sanda
- Za a yi facin titin Abuja zuwa Tafa a kan miliyan N366
Zulum, ya bayyana hakan ne yayin da yake sake tsugunar da mutum 3,800 a ƙaramar hukumar Konduga.
Ya buƙaci dakarun sojim Najeriya da hukumomin tsaro da su ɗauki ƙwararan matakai don kare al’umma.
“Ba za mu iya jure wannan lamari ba yadda ’yan Boko Haram ke kutsawa cikin sansanonin ’yan gudun hijira, suna tafka ta’asa tare da ci gaba da kawo yanayin rashin tsaro,” in ji Zulum.
“Ana samun wasu ‘yan mata da ke cikin ‘yan gudun hijira, suna yin karuwanci da shaye-shayen muggan ƙwayoyi, inda suke ɓata al’adun jihar.
“Ba za mu yarda da irin wannan muguwar ɗabi’a ba,” in ji shi.
Zulum, ya yi gargaɗin cewa gwamnati ba za ta sake lamuntar rashin ɗa’a ba, inda ya yi kira ga manyan jami’an ƙaramar hukumar Konduga da su mara wa ƙoƙarin gwamnatin jihar.
Gwamnan, ya kuma bayyana shirin sake gina ƙauyen Awulari da ke Konduga, tare da bayar da fifikon sake tsugunar da al’ummomin da suka rasa matsugunansu.
Ya kuma bayyana cewa, yunƙurin sake tsugunar da jama’a zai mayar da hankali ne kan al’ummar Sandiya, inda za a gina rukunin gidaje 500 kafin damina mai zuwa.
Don haka ya buƙaci jami’an ƙaramar hukumar Konduga da su ɓullo da dabarun sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar, yayin da gwamnatin ta bai wa waɗanda aka tsugunar kayan abinci da Naira 50,000.
Gwamnan ya yi alƙawarin tallafa wa manoman da ambaliyar ruwa ta shafa tare da gargaɗin waɗanda suka dawo gidajen da ka ba su da su guji sayar da su.
“Dole ne mu tallafa wa manoman da ambaliyar ruwa ta shafa tare da tabbatar da cewa waɗanda suka dawo sun yi amfani da albarkatun da aka samar musu cikin hikima,” in ji Zulum.
Daya daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin, Zainaba Modu, wata bazawara ta yaba wa gwamnan bisa yadda ya samar da gidaje, abinci, da kayayyaki ya samar musu.
Ta ce kuɗaɗen da aka ba su, za zu yi amfani da su wajen kafa sana’o’i domin dogaro da kai.