Wani sabon bincike da aka gudanar a kasar Birtaniya ya nuna cewa rabin ‘yan kasar suna da ra’ayoyin kin jinin Yahudawa.
Rahoton ya nuna cewa ‘yan Birtaniya sun yi ammanar cewa Yahudawa suna ikirarin cewa an yi musu kisan-gilla ne kawai saboda duniya ta rika jin tausayinsu, sannan kuma sun mamaye kafafen watsa labarai na duniya.
Rahoton, wanda wata kungiyar mai suna the Campaign Against Anti-Semitism ta wallafa, ya kara da cewa ‘yan Birtaniya sun yi amanna cewa babu abin da Yahudawa suka fi bai wa muhimmaci kamar neman kudi. Ya kuma nuna cewa kin jinin Yadudawa zai yi kamari a Birtaniya idan ba a yi hankali ba.
Rahoton ya ce ana bayyana yawan Yahudwan fiye da yadda suke a zahiri a kasar, kuma masana na ganin wannan matsar bai kamata a yi wasa da ita ba. An bayyana rohoton da cewa wani abu da ya ce fatan cimma hakan.