’Yan bindiga a Jihar Zamfara sun sanar da sanya haramci a kan ayyukan hakar ma’adinai a yankunan da suke aiki.
Wani shugaban ’yan bindiga a Jihar Zamfara, Shehu Rekeb, ne ya bayyana hakan ne a hirarsa da Aminiya, kan zargin Gwamantin Tarayya cewa masu ayyukan hakar ma’adinai a Zamfara na da hadin baki da ’yan bindiga wurin fasakwaurin makamai.
- A karshe Ganduje ya yi magana a kan Bidiyon Dala
- An cafke dillalin makaman ’yan bindiga a Zamfara
- Yadda dubun mai yi wa yara maza fyade ta cika
- Zamfara: ’Yan bindiga sun yi wa mutane luguden wuta a kasuwa
Amma Shehu Kereb ya shaida wa Aminiya cewa tun kafin umarnin da gwamnatin ta bayar, ’yan tawagarsa sun riga sun haramta hakar ma’adinai a yankunan da suke da karfi.
“Da can Turawa kan je filayen hakar ma’adinai da rakiyar jami’an tsaro, amma yanzun sun daina… Mun hana…. amma makiyaya ba su san yadda ake hakar ma’adinai ba.
“Wadanda kawai muke bari su ne kauyawa talakawa da ba su da abin da za su ci. Mukan bari su shiga wasu wuraren su samu abin da za su rayu da shi. Amma dai mun hana hakar ma’adinai,” inji shi.
Babu amfanin hana tashin jirage a Zamfara
A ranar 2 ga Maris, 2021, Gwamnatin Tarayya ta haramta sauka da tashin jirgi da kuma ayyukan hakar ma’adinai a ta Zamfara.
Amma Gwamna Bello Matawalle ya ce ba ya ganin matakin na Gwamantin Tarayyar zai kawo karshen ayyukan ’yan bindiga.
A ganawarmu ta kwanan nan da Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Kasa na Jihar, Nuraddeen Isah, ya ce hana tashin jiragen ba zai kawo ci gaban tsaron da ake nema a jihar ba, domin a cewarsa, ba abin da ya dace ba ke nan.
Nuraddeen Isah ya ce matakin da Gwamnatin Tarayya ta yanke abin dariya ne saboda a kasar da babu doka ce kawai ake yin hakan.
Ya ce, “Wannan ai kasar zai yi wa illa. Shin suna nufin an keta hurumin kasar ne ko ’yancin diyautarta kasar ke fuskantar barazana? Yaya duniya za ta rika kallon mu?
“Ana nufin a matsayinmu na kasa ba mu da bayanan jiragen da ke karakaina kasar ne? Jiharmu ba ta da filin jirgi ko da dan karami. Wurin saukar helikwafta kawai gare mu, shi ma din a cikin gari yake,” inji shi.