’Yan bindigar da suka sace jami’in Hukumar Hana Fasakwauri ta Ƙasa (Kwastam) a Zariya, Mu’awiyya Gambo Turaki, sun nemi a biya su Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansar shi.
Wata majiya da ke kusa da iyalan jami’in ta ce maharan sun sanar da hakan ne ta hanyar wayar hannu da suka buga wa iyalan nasa.
- NAJERIYA A YAU: 2023: Yadda Tinubu Ya Karbi Batun Takarar Osibanjo
- APC ta lashe zaben Kananan Hukumomin Katsina
Idan za a iya tunawa dai, a ranar Laraba, 30 ga watan Maris, 2022 ce wasu gungun ’yan bindiga suka sace jami’in da dan shi da kuma wasu mutune takwas a anguwar Kofar Gayan Low-cost da ke Zariya.
Sai dai Aminiya ta gano kwana biyu bayan daukar mutanen, ’yan bindigar sun sako dan jami’in Kwastan din mai suna Khalifa, inda aka garzaya da shi asibiti saboda raunukan da ya samu, sakamakon wahalar da ya sha a hannun su.
Har ila yau, bincike ya nuna cewa su ma iyalan sauran mutanen da aka dauke su tare, suna cibgaba da samun kiraye-kirayen waya daga ’yan bindigar don neman kudin fansa.