‘Yan bindiga na neman kudin fansar naira miliyan 100 kan matashin dan siyasar da suka sace a Karamar Hukumar Bogoro a Jihar Bauchi, Musa Markus Masoyi, bayan shafe wata guda a hannunsu.
Aminiya ta gano cewar ‘yan bindigar sun kai farmaki Sakatariyar Kauyen Boi da ke Karamar Hukumar Bogoro a Jihar Bauchi cikin dare, inda suka yi awon gaba da matashin wanda shi ne babban makasudin zuwansu.
- An yi zanga-zanga kan hana Adaidaita Sahu bin wasu titunan Kano
- Tsohon Shugaban China, Jiang Zemin, ya rasu
Wani mazaunin kauyen da bukaci a sakaya sunansa, ya ce ‘yan bindigar sun shiga ne a daidai lokacin da kowa ke barci, suka tafi da wanda aka yi garkuwa da shi zuwa wani wuri da ba a san inda yake ba.
A cewarsa, an yi awon gaba da dan siyasar ne tare da dan uwansa wanda daga baya aka sake shi a cikin daji, inda wasu mutane suka nuna masa hanyar komawa gida.
Kafin sace shi, Markus Masoyi ya taka rawar gani a taron gangamin jam’iyyar PDP da aka kammala domin nuna goyon bayansa ga jam’iyyar a Zaben 2023 mai zuwa.
‘Yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare a wasu jihohin Arewa, inda dubban mutane suka rasa rayukansu, wasu kuma suka sauya matsugunni don tsira da rayukansu.