✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindigar da suka kashe Hakimin ’Yantumaki sun shiga hannu

Dubunsu ta cika a jihar bayan shekara guda da yi wa basaraken kisan gilla a gidasa.

’Yan bindigar dajin da suka yi wa hakimin ’Yantumaki, Alhaji Abubakar Atiku Maidabino, kisan gilla sun shiga hannun hukuma. 

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Katsina, SP Gambo Isa ya tabbatar da cafke mugayen irin.

Idan za a tunawa, a watan Yulin shekarar 202 ne ’yan bindiga suka je gidan hakimin suka kashe daya daga cikin masu gadin gidan, Gambo Isa kafin, sannan suka kashe basaraken.

Daya daga cikin wadanda aka cafke din, wanda mazaunin garin Kagara da ke Karamar Hukumar Matazu ne, ya ce sun je garin tare da wasu da ake nema har yanzu, inda suka yi wannan aika-aika.

Masarautar hakimin na karkashin Karamar Hukumar Danmusa, daya daga cikin kananan hukumomin da ke fama da ayyukan ta’addancin barayin daji a Jihar Katsina.

Karin bayani na tafe…