Yayin da hukumomi da jami’an tsaro suke fama don nemo hanyar da ta fi dacewa wajen magance ta’asar ’yan bindiga da suke ta’addanci a wasu jihohin Arewacin Najeriya, fararen hula masu shiga tsakani da wadanda suke nemo bayanan motsin ’yan bindigar suna samun kansu a tsaka-maiwuya, kamar yadda binciken Aminiya ya gano:
Alhaji Ali (ba sunansa na asali ba ne) yana cikin damuwa da yin nadama lokacin da yake jawabi bayan ya tuna halin da ya shiga.
Ba ya iya ko tsayuwa bayan ya kwashe sama da wata guda tare da sauran wadanda aka kama su aka aje su kamar matattu.
Duk da cewa ba a doke shi ba, amma ya ce baya iya tsayawa da kafafunsa ko yin tafiya a lokacin da aka sake shi mako uku da suka wuce.
“Babu wanda zai iya tsayawa da kafarsa ko ya mike kafafunsa domin kwanciya.
“A zaune muke a tsawon kwanakin da muka yi. Garin kwaki cokali hudu suke ba mu a kullum,” inji shi a kwanaki 33 da ya yi a tsare.
Radadin wahalar da ya sha na nan a jikinsa domin a inda ake ajiye manyan wadanda ake zargi da fashi da makami ko ’yan ta’adda domin yi masu tambayoyi na tsawon makonni ko watanni aka tsare su.
A watan Satumba, aka tsare Ali a biyu daga cikin irin wadannan wurare a Kaduna da Abuja.
Da yake bayani ga Aminiya, Ali ya ce, wannan darasi da ya samu a hannun ’yan sanda ba zai taba mancewa da shi ba har abada.
An yaudare shi ne har ya fada tarkon ’yan sandan bayan wani mutum ya yi masa sharri a matsayin yana hada baki da ’yan ta’adda, mutanen da ya shafe shekara uku yana yakar su ta bayan fage.
“Abin ya faro ne a ranar wata Litinin, wanda ya kira ni a waya ya bukaci mu hadu da shi a bakin hanya saboda yana sauri zai tafi wani wuri. Ban yi zargin komai ba saboda mutum ne da nake magana da shi. Sai na rufe shago na tafi wurin da muka yi za mu hadu,” inji shi.
Bayan sun gaisa da shi har zai juya ya koma sai ’yan sanda suka fito suka kama shi aka saka shi cikin wata mota shi kuma mai ba ’yan sandan bayanai (infoman ’yan sandan) sai ya hau babur ya yi tafiyarsa.
“Sai suka rufe min fuska ba tare da sanin inda za mu ba har sai da sauran wadanda na tarar a tsare suka fada min ai a Kaduna muke,” inji shi.
A cewar Ali, a baya ya taba daukar bindiga inda ya shiga wata kungiyar ’yan ta’adda masu satar shanu a rugagen Fulani a Zamfara, tun kafin karuwar sace-sace a tsakanin matasan Fulani ta kai ga ta’addanci a sanadiyar karuwar miyagun makamai a hannunsu.
Wanda hakan ya sa Ali ya tuba ya koma cikin al’umma ya yi zamansa ya yi aure yana kiwon ’yan dabbobinsa da yake ciyar da iyalinsa da su.
Amma saboda karuwar ta’addanci a yankunan karkara inda yake zaune, sai Ali ya bar yankin gudun kada ’yan ta’addan su kai masa hari ko kuma jami’an tsaro masu farautar ’yan ta’adda su kai masa hari.
“Na kwashe iyalaina muka dawo nan domin cigaba da rayuwa ingantacciya. Na sa yarana a makaranta saboda su yi rayuwa ba irin wacce na yi ba,” inji shi da yake bayani a cikin wani karamin daki daga cikin dakuna uku da yake zaune a yankin Zariya a Jihar Kaduna.
Dan shekara 41, Bafulatanin ya ci gaba da tattaunawa da abokansa da danginsa da sauran mutanensa da suke zaune a cikin dajin da ke mamaye da ’yan bindigar Zamfara da Katsina da Neja.
Wadansunsu ma sun zama jagorori a cikin ’yan ta’adda a yankunan da suke zaune.
Wannan ya sa yake samun bayanan sirri wadanda a maimakon ya yi amfani da bayanan wajen ci gaba da ta’addancisa sai ya ki.
“Na kan bai wa jami’an tsaro bayanan da na samu,” inji shi lokacin da ya tuna bayanan da ya bai wa manyan jami’an sojoji a yankunan da suke fama da rashin tsaro a lokuta dabandaban, wadanda suka yi sanadin kama masu kai wa ’yan ta’addan makamai da kuma dakile yunkurin ’yan bindigar na kai hare-hare a wasu kauyuka.
Ya kuma taka rawa sosai wajen sakin wadansu dalibai da aka sace da kuma tubar wadansu daga cikin ’yan bindigar har da wani wanda tubarsa ta janyo murna sosai a cikin al’umma.
Wani jami’in gwamnati a Jihar Kaduna ya tabbatar da rawar da Ali ya taka kamar yadda ya yi bayani kafin a kama shi.
– Yadda ya kubuta daga hannun jami’an tsaro
A lokacin da yake tsare jami’an tsaro sun kwashe kwanaki suna yi masa tambayoyi a kan dangartakarsa da ’yan ta’addar amma saboda an karbe wayarsa ta hannu a lokacin da aka kama shi ba a ba shi damar yin magana da mutanen da suka san rawar da yake takawa ba, ciki har da wani Janar na soja da wadansu da yake bai wa bayanan sirri a Kaduna da Abuja.
Wahalarsa ta kawo karshe ne bayan ya hadu da wani shugaban Fulani da ke aiki da ’yan sanda a yaki da ’yan bindigar.
Ya san Ali domin sun yi aiki tare wajen tattaunawa da ’yan ta’addar domin samun daidaito.
Ali na kwance a gidansa inda yake jinya ba tare da sanin matakin da zai dauka ba a nan gaba.
– Tsoron za a hallaka shi
Sai dai ya tabbatar wa Aminiya cewa saboda darasin da ya samu yana kokwanton komawa daji saboda kyama da yake fuskanta saboda dadewarsa a tsare da kuma gudun kada makwabtansa da suke zarginsa su hallaka shi.
“Suna ta magana a kan kama ni da aka yi tunda na dawo.
“Ina tsoron suna iya zuwa su kai min hari saboda na ji cewa wai wadansu makwabta suna yada labarin cewa wai an kama ni ne saboda alakata da ’yan ta’adda.
“Kwanan nan aka kashe wani tare da iyalansa saboda zargin yana da alaka da ’yan ta’adda. Saboda haka ya sa nake tsoro,” inji shi ta wayar tarho.
– Masu shiga tsakani suna cikin hadari – Masani
James Barnett, wani masanin bincike a Jami’ar Legas da kuma Cibiyar Bunkasa Dimokuradiyya (CDD), a Abuja, ya ce masu shiga tsakani irin su Ali suna nan a cikin tsaka-mai-wuya.
“Domin masu shiga tsakani irinsu wadanda kila jami’an tsaro suna aiki da su yadda ya dace wajen taimakawa su sansanta da ’yan bindiga domin sakin wadanda aka kama, amma kuma wadansu za su dauki wannan shiga tsakani da suke yi ko kuma wasu jami’an tsaro za su samu lambar wayarsu a cikin wayar wani dan ta’adda sai su dauka suna hada baki ne da ’yan ta’addar.
“Saboda haka masu shiga tsakani irin su suna cikin hadarin ko a kama su ko kuma a kashe su koda kuwa ana san da rawar da suke takawa,” inji shi.
Wani dan jarida da ke bibiyar al’amuran da suka shafi tsaro a Jihar Katsina, Muhammad Danjuma, ya ce ga ’yan ta’adda duk wanda suka kama yana bai wa gwamnati bayanan sirri sunansa matacce.
A wasu lokuta ma zargi kurum na iya sanyawa su zartar wa mutum da hukuncin kisa.
Irin wannan hukunci ne ya fada a kan Alhaji Adamu wanda ke zaune a yankin Kidandan a Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.
Kwanton bauna suka yi masa a kan hanyarsa ta komawa gida daga kasuwa a watan Satumban bana.
Adamu da abokinsa Abdullahi suna aiki da wadansu jami’an tsaro na sirri da shugabannin Fulani domin neman maslaha a kan halin da matasa Fulani suka fada na ta’addanci a dazukan Jihar Kaduna.
Daya daga cikin muggan ’yan ta’adda shi ne Boderi wanda matashi ne dan kimanin shekara 20 wanda mahaifinsa, Alhaji Isyaku sanannen barawon shanu ne a lokacin da yake matashi.
Saboda damuwa da halin da suke ciki na ayyukan ta’addanci na irin su Boderi sai suka fara tattaunawa da wadansu dattawa da suke ganin za su iya taka rawar da za ta kawo karshen ta’addanci a yankinsu.
“Adamu da abokinsa mutanen kirki ne da suke nuna damuwarsu a kan yadda dazuka suka zama filin daga ko yaki, inda babu abin da ake aikatawa a cikinsu in ban da ta’addanci a tsakaninsu da kuma a tsakaninsu da ’yan sa-kai da jami’an tsaro,” inji wata majiya da ta sansu duka.
Wata biyu da suka wuce ne, Abdullahi ya yi takakkiya daga yankinsa a Rijana domin ziyartar abokinsa Adamu domin su ziyarci Alhaji Isyaku da nufin ko zai taimaka ya yi wa fitinannen dansa magana wanda ya zama bala’i ga sauran al’ummar jihar.
Tun farko sun gana da sauran shugabannin Fulani a wasu rugage a yankin, amma duk wanda aka yi wa magana sai ya ba da shawarar a tuntubi Isyaku saboda ana ganin shi kadai ne zai iya yi wa dansa gargadi.
Koda shi da dansa suka bar wurin taron, an tura ’yan bindigar da aka dauki hayarsu don su bi su su kashe su, domin Boderi yana kokwanton abin da ke cikin zukatansu.
Yana zargin su da kasnacewa ’yan leken asiri ne da za su iya juya masa baya ta hanyar fitar wa hukumomi a Kaduna sirrinsa.
Sai dai maharan ba su yi nasara ba domin Allah Ya tarfa wa garinsu Isyaku nono saboda sun samu kubuta a dalilin sauya hanyar da ake zaton za su bi a babur inda da tuni sun sheka barzahu.
Sai dai tsirar ta Adamu wanda ke zaune a dajin Rigachikun a kusa da maboyar Boderi, ba ta yi tsawo ba.
Domin an bi shi aka kashe shi a ranar wata Lahadi a kan hanyarsa ta dawowa daga kasuwar kauye inda aka yi masa kwanton bauna aka harbe shi.
An yi ta dora wa Boderi laifin kisan Adamu ne saboda irin ikirarin da ya yi tare da alwashin kashe shi ta wayar tarho bayan mutanensa sun kasa kashe mutanen biyu.
Tilas Abdullahi ya gudu daga inda aka san shi bayan kisan Adamu, kuma sai da Baffan Boderi mai suna Gana’i ya sa baki aka samu damar da dawo da shanun Abdullahi da Boderi ya kada bayan gaza kama shi Abdullahin.
– Ya sha da kyar a hannun Dogo Gide
Wani mai shiga tsakani don ganin an sako daliban makaranta da mugun dan bindigar nan, Dogo Gide ya jagoranci sacewa da kyar ya tsallake rijiya da baya a hanyarsa ta haduwa da dan bindigar, kamar yadda Aminiya ta samu bayani.
“Sauran ’yan bindigar sun kira Dogo sun fada masa cewa ya kashe mutumin domin yana bai wa jami’an tsaro rahotonsu.
“Ya bayyana hakan ga mutumin amma ya ce babu wata hujja da za ta nuna hakan, don haka ba zai ba shi damar aikata haka ba.
“Da a ce Dogo Gide ya saurari kiraye-kirayen da aka yi masa ta waya da tuni ya gama da mutumin,” kamar yadda wani mai shiga tsakani da ya san karon-battar ya shaida wa Aminiya.
– Dole su iya takunsu
Halin tsaka-mai-wuya da masu shiga tsakani kan tsinci kansu a ciki ya sa dole masu ruwa-da- tsaki su san takunsu kasancewar yadda alakarsu da ’yan bindigar ke iya zama ba mai dorewa ba.
Hakazalika ba su san lokacin da za su iya babewa da jami’an tsaro na gwamnati ba, musamman ga wadanda suka zama daban da wadanda suke aiki da su.
Bernett, ya ce “Su ’yan bindigar sun cika yawan zargi, kuma masu shiga tsakani suna sayar da ransu wajen shiga hadari a duk lokacin da suka amince za su hadu da ’yan bindigar a madadin gwamnati.
“Wadansu ’yan bindigar da ke shiga tattaunawa da gwamnatocin jihohi na fuskantar hadarin kai musu hari daga wata zugar ’yan bindigar ta yadda babu shakka duk wanda suka samu yana kai wa jami’an tsaro labarinsu, to tasa ta kare.
“Matsalar haka take koda ga su Fulani, musamman makiyaya wadanda a cikinsu ne ya kamata gwamnati ta samu masu shiga tsakani ko kuma masu kai mata rahoton kaikomonsu.
“Sai dai hakan ba kawai zai jefa rayuwarsu a cikin hadari ba ne daga cikin Fulani ba, hatta jami’an tsaro ko ’yan sintiri ba za su bar su ba in sun ci karo da su a matsayinsu na Fulani su ma,” inji shi.
Ya ce, “Akwai misalan Fulanin da suke yi wa gwamnati aiki tare da taimakawa wajen kubutar da wadanda aka kama, amma su kansu ba su sha ba, domin ana yi musu kallon ’yan bindiga saboda kasancewarsu Fulani inda ’yan sintiri kan kashe na kashewa da sunan yaki da ’yan bindigar.”
Danjuma, ya ce, “Dole ne mai aikin nemo bayanai ya kare ransa domin duk lokacin da aka rasa amincewa to sakamakonsa mutuwa ne, dalilin da ya sa ba sa bayyanawa ke nan.”
Farauto Mamman
Wakilinmu ya sha wahala a lokacin da ya yi kokarin gano wani fitaccen mai samar da bayanai kan duk wani motsi da ayyukan ’yan bindigar a daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma. Mamman, (an sakaye sunansa na gaskiya), ya taka rawa wajen samun samame da dama da jami’an tsaro suka kai wa ’yan bindiga a Jihar Zamfara, ciki har da wanda aka yi nasarar kama mahaifin Turji, wani kasurgumin dan bindiga a matsayin wani mataki da ake so ya fara sakin mutanen garin da ya kama kuma suke karkashin ikonsa.
Shi da kansa an tuhume shi da laifin zama mai fuska biyu; irin tuhuma da zargin da ake yi wa yawancin masu shiga tsakani.
An zarge shi da barin jama’arsa a cikin daji amma sai ya fito yana tona labarin kungiyoyin adawarsa na ’yan bindigar.
An yi waya da Mamman a tsakiyar watan Satumba inda ya ce zai tattauna da wakilinmu da sharadin samun izini daga manyan hukumomi a jihar tukuna, wanda hakan ya dauki tsawon lokaci kuma bayan wakilinmu ya same shi tare da kokon bara don ba shi damar tattaunawa da shi, sai ya sake kafa masa wani sharadin na sai wakilinmu ya tuntubi wani babba a cikin Kungiyar Miyetti Allah, duk da wakilinmu ya yi masa alkawarin ba zai ambaci sunansa ba.
Bayan Mamman da wakilinmu sun cimma matsaya na haduwa a wata makwabciyar jihar, amma da wakilinmu ya isa inda suka yi yarjejeniya ya kuma kira lambar wayarsa a daren 3 ga Oktoba, sai ya tubure, duk da tabbatar masa da samun izini daga babban kamar yadda ya bukata inda da kyar ya sake yarda su hadu a washegari.
Washegari 4 ga Oktoba wakilinmu ya yi ta kiran shi a waya, amma bai amsa ba inda daga baya ma layin ya daina shiga tun daga lokacin har yau din nan.
Halin da Mamman ya nuna, yana nuni ne da irin yanayin tsoron da masu shiga tsakani sukan tsinci kansu a ciki.
“Suna matukar sayar da ransu; amma duk da haka gwamnati da sauran al’umma sun kasa fahimtar irin halin da suke ciki,” inji Yusuf Anka, wani mai bincike a kan kalubalen harkokin tsaro a Arewacin Najeriya.
Ya ce yawanci masu aikin shiga a tsakanin kauyawa ne da ke da alaka da wadanda ake batun dominsu; in ma alaka ta kasuwanci ko na auratayya.
Sai dai wannan alakar tana dauke da irin tata kasadar, musamman in aka samu rashin mai da himma a kai daga bangaren gwamnati wadda a wasu lokuta ke sanya masu shiga tsakani su tattauna abin da suke bukata amma daga baya a kasa cika musu.
Ya ce irin wannan gazawar tana jefa rayuwar masu shiga tsakanin a cikin hadari a wajen ’yan bindigar.
Kuma wasu lokuta domin dada tattalin alakar, har sukan wuce gona-da-iri wajen yi musu (’yan bindigar) alkawarin abin da hukumomi ba su yi musu alkawari ba.
“Ta kowace fuska ba a fahimce su ba; al’ummar gari sun kasa fahimtar wace rawa suke takawa, jami’an tsaro kuma suna kokwanto a kansu, ’yan sintiri na kishirwar dirar musu, yayin da su-ya-su kuma ’yan bindigar na iya kashe junansu a kowane lokaci,” inji Anka.
Wannan ne dalilin da ya sa da yawan wadanda suka sanya hannu a wannan aiki suke takatsantsan, yayin da wadansu ma suka hakura da aikin shiga tsakanin ta hanyar yar da kwallon mangoro don hutawa da kuda.
– ‘Abin da ya kamata a yi’
Masana harkokin tsaro sun ce hakki ne a kan gwamnati ta tabbatar da amintar da ran mutanen da suka sayar da rayukansu wajen samar da bayanai masu amfani domin kasancewarsa jigo wajen nasarar yaki da ’yan bindigar.
Wani kwararren masanin tsaro, Dokta Kabiru Adamu, ya ba da shawarar fito da wasu tsare-tsare da za su taimaka wajen shimfida wannan dangantaka a tsakanin bangarorin tsaro da na al’umma, inda ya ce tsarin ya kunshi rufa asirin duk wanda ke cikin tsarin da kuma karfafa gwiwa.
“Dadin dadawa kuma alakar a tsakanin bangarori biyun ta zama ta karfafa wa juna ne ba a kalli wani bangare kamar yana yi wa dayan gata ne ba.
“Domin tabbatar da aminci a tsakanin dukkan bangarorin, za a iya samar da wani a tsakani da zai rika lura da aikin da kowane bangare ke yi kuma ya tabbatar kowanne bai saba ka’idar da aka gindaya masa ba,” inji Adamu.
– Dole a samu gaskiya a tsakani – Gumi
Malamin Addinin Musuluncin nan da ya yi fice wajen shiga tsakanin ’yan bindiga don neman sasanci, Dokta Ahmad Gumi ya koka kan rashin gaskiya daga bangaren ’yan siyasa wadanda ya ce rashin sanin hanyoyin magance matsalar da ba ta amfani da matakin soji ne ba ya kawo hakan.
Ya ce magance matsalar na bukatar gaskiya daga bangaren shugabannin siyasa tare da taimaka wa masu nuna kwazo wajen shiga tsakani don sasantawa.
Gumi ya yi zargin tadiye yunkurin da yake yi inda ya ce wadansu fitattun mutane ba sa son ganin ya yi nasara a yunkurin da yake yi.
Duk da ya ce ba zai daina yunkurin da yake yi ba, amma ya ce zai sassauta tare da ja baya kadan da kuma tsara wasu hanyoyin don sabuwar gwamnatin da za ta zo.
Wadansu da suka bayyana ra’ayinsu amma suka nemi kada a bayyana sunayensu, ra’ayinsu ya zo daya da na Gumi, inda suka ce kowane bangare na kokarin a ce shi ne ya yi bajinta, wanda hakan ya fito da gaban da ke tsakanin bangarorin jami’an tsaro da yadda kiyayyar ta haifar da tsaiko game da ayyukan da masu shiga tsakani da masu kai rahoto suke yi.
Wannan rahoto an yi shi ne da tallafin Cibiyar Bunkasa Dimokuradiyya (CDD).
Daga: Abdul’aziz Abdul’aziz Fassarar Mohammed I. Yaba da Ali Ahmed.