’Yan bindiga sun kai hari a wasu kauyukan Karamar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna inda suka kashe mutane da dama, ciki har da shugaban APC na gundumar Aribi, Illiya Auta.
Bayanai daga yankin sun nuna cewa ’yan ta’addan sun kwashi wasu mazauna yankin hade da shanu yayin harin wanda ya faru cikin daren Litinin.
- Hisba ta kama barayin waya 8 a masallaci a Kano
- Yahaya Bello ya zama dan takarar da ya fara sayen fom din APC a kan N100m
Wani ganau a yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, barayin sun yi harbe-harbe a iska bayan shigarsu yankin don firgitar da jama’a.
“A lokacin harin ne aka bindige shugaban APC na Aribi, Mista Illiya Auta har lahira, haka ma wasu da dama sun rasu.
“Barayin sun yi garkuwa da mutane da yawa kana sun jikkata wasu da dama sannan sun kwashi shanu bila adadin,” inji majiyar.
Daga nan, ya yi kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki saboda a cewarsa, ’yan fashin dajin sun mamaye musu kauyuka.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, Gwamnatin Jihar Kaduna da ma Rundunar ’Yan Sandan Jihar ba su ce uffan ba a kan lamarin.
Da wakilinmu ya nemi jin ta bakin mai magana da yawun ’yan sandan Jihar, Mohammed Jalige, bai daga kiran waya da aka yi masa ba.