Wasu ’yan bindiga sun yi wa wasu ‘yan mata masu yi wa kasa hidima (NYSC), fyade a Jihar Akwa Ibom.
Hakan ya auku ne bayan da ‘yan bindigar suka kai hari a wani masaukin masu yi wa kasa hidimar da ke Uyo, babban birnin jihar.
- Barkindo: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da tsohon Babban Sakataren OPEC
- An sake damke fursunoni 551 da suka tsere daga kurkukun Kuje
Bayanai sun nuna cewa, maharan sun kai harin ne cikin dare da misalin karfe 1:00 dauke da bindigogi, inda suka yi wa matan fayade sannan suka kwashe musu wasu muhimman kayayyakinsu da suka hada da kudi da kwamfutoci da wayoyi da sauransu.
A cewar daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa, “Maharan sun zo ne a cikin babur mai kafa uku, ba tare da bata lokaci ba suka shiga aikata abin da ya kawo su. Haka suka bi kofa-kofa suna fasawa da karfi tare da yi mana barazanar za su harbe mu idan ba mu ba su hadin kai ba.
“Ban taba jin labarin faruwar irin haka ba a ko ina a kasar nan, inda bata-gari za su shiga su yi wa masu hidimar kasa fyade su kuma kwashe musu kaya ta hanyar nuna musu bindiga,” inji ta.
Wani mazaunin yankin mai suna Bassey Offiong, ya ce da ya fahimci abin da ke faruwa sai ya hanzarta kiran ofishin ‘yan sanda na Ikot Akpanabia da ke kusa da su, amma ba su tashi zuwa sai bayan da barayin suka yi abin da suka ga dama suka tafi.
Da aka nemi jin ta bakinsa dangane da al’amarin, Jami’in Hulda da Jama’a na ‘Yan Sandan Jihar, SP Odiko Macdon, ya ce ba shi da cikakken bayani a kan bin da ya faru, “….amma zan bincika in gani,” inji shi.