✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘’Yan bindiga sun yi wa daliban da suka sace ciki’

’Yan bindigar sun aure dalibai matan bayan shafe tsawon lokaci a tare da su.

’Yan bindiga sun yi wa wasu daga cikin dalibai mata da suka yi garkuwa da su a Sakandiren Gwamnati (FGC) da ke Birnin Yawuri a Jihar Kebbi ciki, bayan aurensu da suka yi.

Shekarar 2021 da ta gabata ita ce mafi muni inda aka sace dalibai da dama.

Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa adadin dalibai mata 1,440 ne aka sace daga makarantu 25 da ke fadin Najeriya.

A ranar 17 ga watan Yunin 2021, yaran kasurgumin dan bindigar nan Dogo Gide, suka farmaki Kwalejin Birnin Yauri da ke Jihar Kebbi, inda suka sace dalibai da malamai da dama.

Bayan shafe kwanaki da sace su, maharan sun kira iyayen daliban tare da shaida musu cewar sun aurar da su.

Wasu daga cikin iyayen sun bayyana yadda ’yan bindigar suka aike musu da bidiyon yadda suka aurar da ’ya’yansu.

Har wa yau, wata majiya ta tabbatar wa da Aminiya cewar an aurar da daliban ga ’yan bindiga kuma tuni wasu 13 daga cikinsu suka samu juna biyu.

Daliban mata an aurar da su ga ’yan bindiga da wasu mazauna kauyukan da Dogo Gide ke karkashin ikonsa a jihohin Neja da Zamfara.

Wata majiya wadda ta yi ruwa da tsaki wajen sakin wasu a baya, ta shaida wa wakilinmu cewar ’yan bindigar sun saki wasu dalibai mata uku a cikin watan Janairu, kuma kowanensu ta dawo da juna biyu.

“Guda 11 suna can har yanzu, 10 daga cikinsu an aurar da su har da yaro daya ma. An saki guda uku a cikin watan Janairu kuma sun dawo da ciki a tare da su,” cewar majiyar da ta bukaci a sakaya sunanta.

Aminiya ta rawaito yadda a watan Oktoban 2021 kasurgumin dan bindigar ya ki sakin wasu dalibai mata duk da karbar kudin fansa da kuma sakin wasu yaransa biyu da aka yi.

Da ya ke jawabi yayin shiri a kan yaran da ba sa zuwa makaranta a Birnin Kebbi, Minista a Ma’aikar Ilimi, Emeka Nwajiuba, ya tabbatar da cewar har yanzu ’yan bindigar na rike da dalibai 14.

Kazalika, Mai Bai Wa Gwamnan Jihar Kebbi Shawara Kan Sha’anin Tsaro, Garba Rabiu Kamba, ya shaida wa Aminiya a wayar tarho a satin da ya gabata cewar ’yan bindigar ba su saki dalibai 14 da ke hannunsu.