’Yan bindiga sun yi garkuwa da ’yan Kasuwar Kantin Kwari da ke Jihar Kano 18 a kan hanyarsu ta zuwa fatauci a yankin Kudancin Najeriya.
A Jihar Kogi ne ’yan bindiga suka tare motar ’yan kasuwar suka yi awon gaba da su zuwa cikin jeji, a lokacin da ’yan kasuwan ke hanyarsu ta zuwa garin Aba na Jihar Abiya domin sayen hajoji.
- Nuna tsiraici: Bidiyon sabuwar wakar Hausa ya ta da kura a intanet
- Tsadar hatsi na neman fin karfin mutane a Kaduna
- Jiragen yaki sun yi wa Boko Haram ruwan wuta a Borno
- Tashar Buhari: Da N30 sai a kai ka har gida a Kano
Manajan-Daraktan Hukumar Gudanarwar Kasuwar Kantin Kwari, Alhaji Abba Bello ya tabbatar wa Aminiya cewa, “’Yan kasuwa 18 ne aka yi garkuwa da su, mutum 12 daga cikinsu mun tabbatar da sunayensu, amma muna ganin sun kai mutum 18.
“Suna hayarsu ta zuwa fatauci a garin Aba na Jihar Abiya ne ’yan bindiga suka tare motarsu a kan babbar hanyar Lokoja zuwa Okene a Jihar Kogi.
“Mutane na cewa wadanda aka yi garkuwa da su za su kai mutum 20 ko fiye da hakan, amma adadin da muka iya tabbatarwa shi ne mutum 18,” inji Alhaji Bello.
Aminiya ta tambaye ko ’yan bindigar sun tuntubi iyalan wadanda aka yi garkwar da su ko neman kudin fansa, amma ya ce babu wani bayani game da hakan.
Amma wata majiya ta ce da farko mar garkuwa da mutanen sun bukaci a biya kudin fansa Naira miliyan 50 daga iyalan ’yan kasuwar, kafin daga baya su rage zuwa miliyan 27.
’Yan kasuwar sun bar Kano ne a ranar Lahadi da don zuwa garin Aba a Jihar Abia amma suka gamu da kaddarar.
Kananan ’yan kasuwa da dama a Kasuwar Kantin Kwari kan yi tafiya a motoci zuwa garin Aba, cibiyar kasuwancin Jihar Abiya, domin su sayo yadi ‘Dan Aba.’