✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban CAN a Nasarawa

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Kuniygar Kiristoci Najeriya (CAN) reshen jihar Nasarawa Bishop Joseph Masin. Masu garkuwan dauke da muggan makamai sun kutsa…

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Kuniygar Kiristoci Najeriya (CAN) reshen jihar Nasarawa Bishop Joseph Masin.

Masu garkuwan dauke da muggan makamai sun kutsa gidan Bishop Joseph da tsakar dare suka yi awon gaba da shi.

Tsohon sakataren CAN na jihar Nasarawa Yohana Samari ya ce lamarin ya auku ne a unguwar Bukan Siri da ke garin Lafiya.

Kwashinan ‘yan sandan jihar Bola Longe ya shaida wa wakilinmu cewa ‘yan bindigar sun tafi da malamin addinin ne a kan babur.

Har yanzu babu labarin inda Bishop Joseph din ya ke.

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce suna bin sawun bata garin domin kubutar da Bishop Joseph.