Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 15 da kashe biyu a unguwar Mangwaro jihar Neja wanda take makwabtaka da jihar Kaduna.
Majiyarmu ta gano cewa, an yi garkuwa da mutanen ne lokacin da suke hanyarsu ta zuwa jihar Kaduna, a wata unguwa da take da iyakar jihar Neja da Kaduna.
Kwamishinan watsa labarai na jihar Neja Danjuma Sallau, ne ya sanar da hakan inda ya ce, mutum 10 ga aka yi garkuwa da su ‘yan garin Gwada ne a Karamar hukumar Shiroro yayin da sauran biyar din ‘yan karamar hukumar Munya ne.
Jama’ar kananan hukumomin Munya da Shiroro da Rafi na fargaba da bullar ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane, sakamakon makwabtakar su da jihar Zamfara.