✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace lakcara da yara 2 a Zariya

Wasu ’yan bindiga a ranar Asabar sun kutsa rukunin gidajen malamai a Kwalejin Kimiya da Kere-kere ta Nuhu Bamalli da ke Zariya inda suka yi…

Wasu ’yan bindiga a ranar Asabar sun kutsa rukunin gidajen malamai a Kwalejin Kimiya da Kere-kere ta Nuhu Bamalli da ke Zariya inda suka yi garkuwa da wani lakcara da ’ya’yansa biyu suka kuma harbi wani mutum daya.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar lamarin da ta ce ya auku ne da misalin karfe 10.00 na daren ranar Asabar.

Sanarwar da Jami’in Hulda da Al’umma na rundunar, ASP Muhammad Jalige ya fitar ta ce an garzaya da wanda ya samu raunin zuwa Asibitin Koyarwa a Jami’ar Ahmadu Bello inda ya ke samun kulawa ta kwararru na lafiya.

ASP Jalige ya ce: “mun yi wa makarantar tsinke da jami’anmu kuma muna kokarin ceto wadanda maharan suka yi awon gaba da su”.

Aminiya ta tuntubi kakakin makarantar, Abdallah Shehu, domin karin bayani.

Ya shaida mata cewa yana halartar wani taro ne amma ya yi alkawarin waiwayar wakilinmu da zarar ya samu dama.