Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da Kansilan dake wakiltar mazabar Ewohimi a Karamar Hukumar Esan ta Kudu maso Gabas ta jihar Edo, Hon Israel Inyanabor.
Rahotanni sun ce an yi garkuwa da Kansilan ne a ranar Talata akan hanyar Ewatto-Ubiaja-Okhuesan kusa da kogin Ena na karamar hukumar.
- An cafke masu garkuwa da mutane a Edo
- An ware kwanaki 7 don farautar ‘yan ta’adda a Edo
- An sace Shugaban Karamar Hukuma da wasu mutum 13 a Edo
An kuma gano cewa an sace Israel a daidai wurin da aka yi garkuwa da wani malamin makaranta, Mista Aluola da matarsa a ranar Litinin.
Mista Israel dai na tsaka tuki ne a kan hanyar Ewohimi lokacin da wasu ’yan bindiga ba zato ba tsammani suka fito daga daji suka fara harbe-harbe, wanda hakan ya tilasta mishi tsayawa.
Daga nan ne masu garkuwar suka sace shi zuwa cikin daji inda suka saba garkuwa da mutane.
Aminiya ta gano cewa a cikin sa’a 48 an sace mutane uku, Mista Aluola da matarsa da Inyanabor a kan hanyar.
A yanzu haka dai mazauna yankin na rokon a tura rundunar tsaron hadin gwiwa zuwa yankin saboda bata-garin da suka addabe su.
Sai dai duk yunkurin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Chidi Nwanbuzor game da faruwar lamarin ya ci tura.