Kimanin fasinjoji 18 ne suka fada tarkon masu garkuwa da mutane a yayin da ’yan bindiga suka tare musu hanya a Jihar Neja.
Wannan sabon hari na ’yan bindigar ya auku ne ranar Lahadi a kauyen Yakila da ke Karamar Hukumar Rafi ta Jihar.
- Wata 5 da karbar kudade, har yanzu Rarara bai yi wakar Buhari ba
- Har yanzu ba a gano asalin Coronavirus ba – WHO
- Kifi mai tsawon inci 7 ya makale wa masunci a makogwaro
Shugaban Hukumar Bayar da Agaji na Jihar Neja, Mallam Ibrahim Inga, ta tabbatar da aukuwar lamarin a wata zantawa da ya yi da wakilinmu ta hanyar wayar tarho.
Inga wanda ya kamo hanyarsa daga garin Kagara domin sabunta rajistarsa ta jam’iyyar APC, ya ce ya kai ziyara wurin da ’yan bindigar suka ci karensu babu babbaka.
Ya ce sun riski wata mata da danta wacce ’yan bindigar suka tafi suka bari amma sun yi awon gaba da fasinjoji goma sha takwas.
“Abin da zan iya fada a yanzu shi ne mun ceto wata mata da jaririnta kuma a yanzu haka mun kamo hanyar birnin Minna tare da ita a mota.”
“Ta shaida mana cewa ’yan bindigar sun tare musu hanya ne sannan suka yi awon gaba da fasinjoji 18 da suke tare.”
“Babu wani jami’in gwamnati a cikin wadanda aka yi garkuwa da su amma daga haka babu wani karin bayani da zan yi domin kuwa matar tana cikin dimuwa saboda haka ba za mu iya ci gaba da tambayarta ba,” in ji Inga.
Sai dai ya sha alwashin waiwayar wakilinmu domin shigar da karin bayani.
Yayin da aka nemi jin ta bakin Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, Wasiu Abiodun, bai amsa kiran wayarsa ba ballanta bayar da amsar sakon kar ta kwana da aka tura masa.