✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace daliban kwaleji a Kaduna

Sa'o'i bayan Shugaba Buhari ya ba sojoji wa'adin magance satar mutane da kuma harbe duk wanda ke dauke da bindiga.

’Yan bindiga sun sace daliba a cikin dare a wata makaranta ke cikin garin Kaduna.

Majiyoyi a Kwalejin ta Horon Samar da Kayan Kula da Gandun Daji ta Tarayya (FCFM), Afaka, da ke unguwar Mando sun ce ana fargabar ’yan bindigar sun yi awon gaba da kusan rabin dalibai mata da ke makarantar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda reshen Jihar Kaduna, Muhammad Jalige ya shaida wa Aminiya cewa: “An yi garkuwa da su ne a cikin dare, amma babu bayani game da yawansu, kuma ba zan iya cewa ba ko dukkansu mata ne”.

Ya kuma ce suna aiki tare da sojoji wajen bin sawun masu garkuwar da kuma kubutar da daliba.

Shi ma da yake tabbatar da aukuwar lamarin,  Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan ya ce sun riga sun isa kwalejin don tantance hakikanin abun da ya faru.

Bayan luguden wuta da maharan suka yi da tsakar dare sannan suka yi awon gaba da daliban, an wayi garin Juma’a da ganin iyayen dalibai da mazauna sun yi dafifi a makarantar da ke cikin garin Kaduna.

Mazauna sun tabbatar da jin karar hare-hare a cikin dare, amma sun dauka daga Kwalejin Horas da Kananan Hafsoshin Soji ta NDA ne.

Mando unguwa ce mai makwabtaka da NDA da Babban Filin Jirgin Sama na Kaduna a bangare guda, da kuma Barikin Sojin Sama daga daya bangaren.

Aminiya ta kuma gano cewa tuni jami’an tsaro sun isa makarantar sun kuma fara bincike yayin da jirgi ke shawagi don gano inda aka bi da wadanda aka sacen.

Harin na zuwa ne sa’o’i kadan bayan umarnin Shugaba Buhari ga jami’an tsaro cewa su bindige duk wanda aka gani dauke da bindiga ba bisa ka’ida ba.

A lokacin ne kuma ba wa Manyan Hafsoshin Tsaro wa’adin mako shida, wato kafin faduwar damina, su shawo kan matsalar ’yan bindiga da suka addabi yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Gabanin harin Buhari ya yi alkawarin cewa sace dalibai mata 279 da ‘yan bindiga suka yi a makarantar sakandaren GGSS Jangebe, Jihar Zamfara, shi ne zai zama karon karshe da aka yi garkuwa da dalibai a Najeriya.