’Yan bindiga sun kai hari a wata makarantar firamare inda suka yi awon gaba da dalibai da ba a san adadinsu ba da kuma malamai a safiyar ranar Litinin a Jihar Kaduna.
Maharan sun yi garkuwa da daliban da malamai uku ne a makarantar firamaren UBE da ke unguwar Rama mai nisan kilimita biyar daga garin Birnin Gwari.
- ’Yan bindiga sun sace limami da mutum 10 a Suleja
- Mun kaddamar da yaki da ’yan bindiga —Gwamnan Binuwai
- Matar aure ta kashe danta, ta kona mijinta
- Farashin kayan gwari ya fadi warwas a Kano
Mai Unguwar Rama, Abdulsalam Adam ya shaida wa Aminiya ta waya cewa, “Na samu labari cewa sun tafi da malamai uku da dalibai amma muna kokarin tabbatar da ainihin abin da ya faru tare da ’yan banga, sauran jama’a kuma sun bi sahun ’yan bindigar.
“Yanzu muna makarantar muna duba dazuka saboda wasu yaran sun tsere sun shiga dazuwa. Yanzu ba za mu iya cewa yara nawa ne aka tafi da su ba,” ya kuma ce maharan sun kai farmakin ne a kan babura 12.
Wani mazaunain garin, ya ce: “Daya daga cikinmu ya ga dansa sun dauke shi a kan babur.
“Mutane da yawa sun yi ta maza sun bi sawun maharan; Yanzu muna marantar; mun sa a kira jami’an tsaro amma ba su riga sun karaso ba,” a ceawrsa.
Mazauna garin Rama sun shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar auka wa makarantar ne da misalin karfe 9 safiyar Litinin a yayin da dalibai ke isa makarantar.
Shi kuma wani mazaunin garin Birnin Gwari ya ce ’yan uwansa na daga cikin malaman da aka yi garkuwa da su.
Sai dai Kansilan Rama, Aliyu Isa ya ce malamai uku ne ’yan bindiga suka dauka, banda dalibai, kuma maharan sun kuma kai farmaki a wani kauye inda suka dauke mutum biyu suka kuma saci shanu biyu.
Karo na uku ke nan cikin kwana huku da ’yan bindiga ke kai wa makarantu hari a Jihar Kaduna.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce sun samu rahoton garkuwa da daliban da malamansu, “Kuma rahotannin wucin gadi sun nuna abin ya faru ne a makarantar firamare ta LEA da ke kauyen Rema a Karamar Hukumar.”
Aruwan ya ce suna ci gaba da tattara bayanai game da sace daliban sannan ya yi alkawarin cewa Gwamnatin Jihar za ta fitar da cikakken bayani “ba da jimawa ba”.
Harin na makarantar firamaren na zuwa ne washegarin wanda ’yan bindiga suka yi yunkurin garkuwa da dalibai 307 a makarantar kwana ta GSSS Ikara a Jihar Kaduna, amma sojoji suka fatattake su.
A ranar Lahadi ’yan bindiga sun kai hari rukunin gidajen ma’aikatan Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama (FAAN) da ke Karamar Hukumar Igabi.
Idan ba a manta ba, ranar Alhamis da dare ’yan bindiga sun kai hari a Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya (FCFM) da ke Afaka a Karamar Hukumar ta Igabi, inda suka yi garkuwa da dalibai 30 — mata 23, maza 16, yayin da sojoji suka kubutar da dalibai da malamai 180.
’Yan bindigar da suka dauke dalibai 39 din na namen a ba su kudin Naira miliyan 500, yayin da Gwamna Nasir El-Rufai kuma a wata hira da aka yi da shi ya yi watsi da biyan kudin fansa don kubutar da daliban.