’Yan Sanda sun tabbatar da garkuwa da wata budurwa mai shekara 18 da sanyin safiyar Juma’a a unguwar Gangaren NEPA da ke garin Birnin Kebbi, Jihar Kebbi.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kebbi, DSP Nafi’u Abubakar ya tabbatar wa manema labarai hakan a Birnin Kebbi.
- Shekara 25 bayan gwajin rigakafin Pfizer a Kano, har yanzu tsugune ba ta kare ba
- Babu maganar karin kudin man fetur zuwa N212 – NNPC
Abubakar ya ce ’yan sanda na kokarin ganin an kubutar da budurwar daga lamarin da ya ritsa da ita.
Ya kuma bukaci jama’a da su taimaka da bayanan da za su taimaka wajen samun nasarar ceto baiwar Allar.
Rundunar ta kuma roki jama’ar jihar da su kai wa jami’an tsaro rahoton duk wata alama da ke da alaka da barazanar tsaro don daukar matakin da ya dace.