✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da babban ma’aikaci a jihar Zamfara

Wasu mutane da ake zargi ‘yan bindiga ne sun sace mutum biyar ciki har da wani babban ma’aikacin gwamnati a kauyen Kanoma na karamar Hukumar…

Wasu mutane da ake zargi ‘yan bindiga ne sun sace mutum biyar ciki har da wani babban ma’aikacin gwamnati a kauyen Kanoma na karamar Hukumar Maru da ke Jihar Zamfara.

Mazauna sun shaida wa Aminiya cewa, mahara sun shigo kauyen ne da misalin karfe 2 na dare inda suka kutsa gidan Darektan na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar kuma suka yi awon gaba da shi.

“Daga nan sun yi awon gaba da wasu iyalan tsohon Mataimakin Magatakardan Majalisar Dokokin Jihar kuma suka arce da su cikin dokar daji,” inji wani mutumin kauyen mai suna Ibrahim.

A baya bayan ne wata Kungiyar matasan Arewa ta AYF ta sanar da cewa hare-haren ‘yan bindiga ya mayar da kimanin mata dubu 22 zawarawa sakamakon mutuwar mazajensu a jihar Zamfara.

Shugaban Kungiyar, Gambo Ibrahim Gujungu, shi ya sanar da hakan da cewa hare-haren ‘yan bindigar ya mayar da yara dubu 44 marayu a jihar.

Ya ce yana da wahala a yi kwana guda ba tare da an samu aukuwar harin masu ta’adar ba a jihar.