✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi awon gaba da takardun jarabawar NECO a Kaduna

’Yan fashin sun dauka kudi ne makare a cikin jakar takardun jarabawar.

An shiga firgici a Unguwar Sarki da ke garin Kaduna, yayin wasu ’yan bindiga suka kai samame tare da yin awon gaba da takardun jarabawar NECO a ranar Juma’a.

Aminiya ta gano ’yan bindigar sun farmaki Makarantar Sakandaren Gwamnati, wadda ake yi wa lakabi da ‘Black and White’ ne yayin da dalibai ke jiran a fara jarabawar; su kuma suka yi awon gaba da jakar da takardun suke ciki, sun dauka kudi ne.

  1. Buhari zai gina gidajen yari a Kano da wasu jihohi
  2. Buhari ya yi alkawarin dawo da martabar Arewa —Matawalle

Rahotanni sun bayyana dalibai da malamai sun shiga rudani inda suka yi zaton cewa masu garkuwa da mutane ne suka kawo hari makarantar.

Tsohon kansilan Unguwar Sarki, Zubairu Shan’una ya shaida wa Aminiya cewa ’yan fashin sun biyo jami’ar NECO da ta dauko takardun jarabawar daga banki har zuwa harabar makarantar.

A cewarsa, ’yan bindigar sun yi zaton kudi ne a cikin jakar da aka dauko, sai suka ritsa ma’aikaciyar cewa ta ba su jakar ko su harbe ta da bindiga.

Wani dalibi ya ce sai da ’yan bindigar sun shiga makarantar sannan suka yi awon gaba da jakar takardun jarabawar.

“Takardun jarabawar kadai suka dauka, ba su taba kowa ba, sun dauka kudi ne a cikin jakar,” a cewarsa.

Har wa yau, wata dalibar ajin karshe ta ce ’yan fashin sun tsare malaman makarantar sannan suka bukaci a ba su jakar.

“Sai bayan tafiyarsu kowa ya tsere an dauka ’yan bindiga ne,” a cewarta.

Kokarinmu na jin ta bakin shugabannin makarantar ya ci tura, inda suka bayyana cewar ba su da damar yin magana da ’yan jarida.

Kwamishinan Ilimin Jihar Kaduna, Dokta Shehu Makarfi bai daga waya ba balle a ji ta bakinsa kan faruwar lamarin.