✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga Sun Yi A won Gaba da Budurwa A Zariya

’Yan bindiga sun yi awon gaba da wata budurwa tare da kashe mutum daya a Karamar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna. Da misalin karfe 2.00…

’Yan bindiga sun yi awon gaba da wata budurwa tare da kashe mutum daya a Karamar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna.

Da misalin karfe 2.00 na dare kafin wayewar garin ranar Talana ne maharan suka far wa kauyen Dorayi da ke karamar hukumar, suka harbe wani mai suna suna Abdullahi Alhaji Ardo, sannan suka tafi da budurwar mai suna Mariya Alhaji Ardo da karfin tsiya.

Idan za a iya tunawa kauyen Dorayi ya fuskanci irin wannan matsala a ’yan makonnin baya.

Aminiya ta kawo rahoton yadda aka yi garkuwa da mai unguwar kauyen, kafin daga bisani asiri ya tonu, aka kama wasu sojoji da dan banga sun je karbar kudin fansar basaraken.