✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sako shugaban PDP na Legas

Maharab sun bukaci a biya su miliyan 200 a matsayin kudin fansa kafin sakin shugaban.

Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Legas, Mista Philip Aivoji, ya kubuta daga hannun ‘yan bindigar da suka sace shi bayan shafe kwana hudu a hannunsu.

Kakakin jam’iyyar PDP na Jihar Legas, Alhaji Hakeem Amode, ne ya tabbatar da sakin Shugaban Jam’iyyar, Mista Philip Aivoji da ‘yan bindiga suka sace.

Amode, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Legas a ranar Litinin.

“Muna amfani da wannan dama don gode muku game da addu’o’i; kuma muna godiya game da nuna kulawarku,” in ji Amode.

An sace Aivoji ne ranar Alhamis a unguwar Ogere da ke Ogun kan titin Ibadan zuwa Legas.

Shugaban jam’iyyar yana kan hanyarsa ta dawowa daga taron PDP na shiyyar Kudu Maso Yamma da aka gudanar a Ibadan da ke Jihar Oyo a ranar Alhamis.

Tun da farko maharan sun kira iyalansa, inda suka bukaci a biya su miliyan 200 a matsayin kudin fansa.

Sai dai Amode bai tabbatar da ko an biya kudin kafin sakin shugaban ba.

Jam’iyyar ta gode wa jami’an tsaro da hukumomin gwamnati da suka taimaka wajen sako shugaban nata.