✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sako Sarkin Jaba

An sakon sarkin mai shekara 83 bayan kwana biyu a hannun masu garkuwa.

’Yan bindiga sun sako Sarkin Jaba, Danladi Gyet Maude da suka yi garkuwa da shi a cikin makon nan.

’Ya bindiga sun sako Sarkin Jaba, wanda babban basarake ne a ranar Laraba, kwana biyu bayan sun yi garkuwar da shi a gonarsa.

Majiyarmu a fadarsa ta Kpok Ham da ke garin Kwoi a Jihar Kaduna, ya tabbatar mana cewa an sako Sarkin Jaba ne da misalin karfe 9.30 na dare, amma bai yi karin bayani ba.

Sakin Sarkin Jaba mai shekara 83 a duniya zuwa fadarsa ta Kpok Ham da ke garin Kwoi, a Karamar Hukumar Jaba ta sa an yi ta murya a masarautar.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da Sarkin Jaba ne a gonarsa da ke kan hanyar Kwoi zuwa Keffi a Jihar Nasarawa.