Kimanin mutum 51 da ake sace a yankin Millenium City da ke Jihar Kaduna sun shaki iskar ’yanci bayan shafe makonni a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da su.
Mazaunan Unguwar Keke B 35 da kuma na Unguwar Sabon Gero 16 da ’yan bindigar suka sace sun dawo matsugunansu ne a ranar Asabar.
- NLC ta bukaci Buhari ya kara wa ma’aikata albashi da kashi 50
- Ango ya fasa auren amaryarsa ana tsaka da biki saboda gajartarta
Bayanai sun ce jama’ar Unguwar Keke B 35 da aka sace sai da suka biya kudin fansa na naira miliyan 2 gabanin su kubuta.
Sai dai wakiliyarmu ta ruwaito cewa, babu wata fansa da aka biya gabanin sako mazauna Unguwar Sabon Gero 16 kamar yadda jagoran rundunar hadin gwiwa da ke yankin, Uwasu Yunusa ya tabbatar.
Haka kuma, wani jagoran al’umma da ke Unguwar Keke B da ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da biyan fansar naira miliyan biyu da mutanensa suka yi gabanin su shaki iskar ’yanci.
Ya ce, “wadanda abin ya shafa sun dawo unguwar Keke B a ranar Asabar, kuma an yi maraba da dawowarsu fuskoki cike da annuri.
“Sai dai abin takaici har yanzu mutum guda yana hannun ’yan bindigar da suka dage cewa sai iyalansa sun siya musu babura biyu kafin a sako shi.”
Aminiya ta ruwaito cewa, a karshen watan Yulin da ya gabata ne maharan suka far wa unguwar Keke B misalin karfe 9.00 na dare suna shiga gidaje su tisa keyar mutane zuwa cikin daji.
Wani mazaunin unguwar Keke A da ya zanta da Aminiya a lokacin faruwar lamarin, ya ce cikin wadanda aka sace har da surukarsa da wasu ma’aurata da dansu na goye.