✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sako karin ’yan makarantar Bethel mutum 6

An sako su ne da yammacin ranar Juma’a.

’Yan bindiga sun sako karin daliban Makarantar Bethel Baptist da ke Kaduna su biyar tare da wata malamarsu ranar Juma’a.

Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya ta Baptist (NBC), Dokta Israel Adelani Akanji ne ya tabbatar da sako su a wani gajeren sakon kar-ta-kwanan da ya aike wa wakilin Aminiya da yammacin ranar Juma’a.

Ya ce, “Mun gode wa Allah. Biyar daga cikin daliban makarantar Bethel Baptist da wata malamarsu (su shida kenan) sun kubata da yammacin yau [Juma’a], takwas ga watan Oktoba.

“Muna godiya ga Allah, kuma muna kyautata zaton sauran dalibai hudun da suka rage su ma za su kubuta. Muna godiya da addu’o’inku,”inji Akanji.

Kimanin kwana 97 kenan da sace daliban daga makarantar ta Bethel, kuma har yanzu akwai kimanin dalibai hudu a hannunsu.