✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sako daliban makarantar Bethel 15 a Kaduna

An dai sako daliban ne da daren ranar Asabar.

’Yan bindiga sun sako 15 daga cikin daliban makarantar sakandiren Bethel da ke Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna.

A baya dai ’yan bindigar sun sako 28 daga cikin daliban ranar Lahadi, 25 ga watan Yulin 2021, bayan rahotanni sun nuna an biya diyyar Naira miliyan 50, kwana 20 da sace su.

Daliban dai wadanda yawansu ya kai kimanin 121, a cewar Shugaban Ikilisiyar Baptist ta Kaduna wanda kuma shi ne mai makarantar, Rabaran Ishaya Jangado an sace su ne ranar biyar ga watan Yulin 2021.

A ranar dai ’yan bindiga suka yi wa makarantar da ke garin Damishi da ke kan hanyar Kaduna zuwa Kachia dirar mikiya da misalin karfe 2:00 na dare sannan suka tafi da daliban.

To sai dai Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Jihar Kaduna (CAN) Rabaran John Hayab ya tabbatar da sako 15 daga cikin daliban da daren ranar Asabar.

SAURARI: Abin Da Ya Sa Hukumomi Suka Kasa Shawo Kan Kwalara

%d bloggers like this: