’Yan bindiga sun saki ɗaliban makarantar Kuriga 287 da suka sace a Jihar Kaduna.
Ɗaliban sun shaƙi iskar ’yanci ne bayan shafe kimanin kwanaki 16 a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da su.
Gwamna Uba Sani ne ya sanar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook da tsakar dare wayewar gari yau Lahadi.
Gwamnan wanda bai yi ƙarin bayani kan yadda aka saki ɗaliban ba, ya dai gode wa Shugaban Kasa Bola Tinubu bisa tabbatar da ganin an sako ɗaliban ba tare da an “cutar da su ba.”
Haka kuma, ya miƙa godiya ta musamman ga mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan sha’anin tsaro, Malam Nuhu Ribadu da rundunar sojin kasa dangane da rawar da suka taka wajen cimma wannan muhimmiyar nasara.
Kazalika, ya miƙa godiyarsa ga ɗaukacin al’ummar Nijieriya da suka bayar da gudunmawar addu’o’i don ganin ɗaliban sun kuɓuta cikin koshin lafiya.
Aminiya ta ruwaito cewa, a farkon wannan wata na Maris ne wasu ’yan bindiga suka yi wa makarantar firamare da ƙaramar sakandiren Kuriga — da ke yankin ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna — ƙawanya tare da awon-gaba da wasu ɗalibai kimanin 287 da malaminsu guda ɗaya, kodayake shi malamin ya samu kuɓuta.
A lokacin da gwamnan jihar Uba Sani ya kai ziyara garin, malamin da ya kuɓuta Abubakar Isah ya shaida masa cewa, maharan sun zo makarantar ne daidai lokacin da aka kammala taron ɗalibai wato Assembly.
Malamin ya ce an ɗauki ɗaliban makarantar sakandire kimanin 187, sai kuma na Firamare 125, aka kaɗa su daji, sai dai malamin ya ce da suka fara tafiya shi da wasu ɗalibai kimanin 25 sun kuɓuta.
Tun bayan sace ɗaliban ne dai Shugaba Tinubu ya bai wa hukumomin tsaron ƙasar umarnin ganin an kuɓutar da ɗaliban, sai dai ya ce duk rintsi babu ko sisin kobo da za a biya a matsayin kuɗin fansa.