✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun saki hoton jaririyar da fasinjar jirgin kasan Abuja ta haifa a hannunsu

An ga hoton jaririyar da mai jegon ta haifa a hannun masu garkuwa a mutane tana barci.

’Yan bindigar da suka sace mutane a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun fitar da hoton jaririyar da wata mai juna biyu daga cikin fasinjojin jirgin ta haifa a hannunsu.

Bayan wata daya da yin garkuwa da mutanen ne dai ’yan ta’addar suka fitar da hotunan mutanen, kusan su 60.

Daga bisani a ranar Laraba suka fitar da hoton jaririyar da mai jegon ta haifa, tana barci a cikin majanyi.

Bayanai sun nuna a lokacin da aka yi garkuwa da su, matar da ta haihu a hannun ’yan bindigar, tana dauke da tsohon ciki wata takwas.

Ana zargin ’yan kungiyar Ansaru — wani bangare da ya balle daga kungiyar Boko Haram – ne suka yi garkuwa da matafiyan.

A ranar 28 ga watan Maris ne aka kai harin bom kan jirgin kasan da ya taso daga Abuja da misalin karfe 6:10 na yamma zuwa Kaduna.

A harin ne aka kashe mutum takwas, aka yi garkuwa da kimanin 60, ragowar fasinjojin kuma suka sha da kyar.