’Yan bindiga sun saki Mai Garin kauyen Guga da ke Karamar Hukumar Bakori ta Jihar Katsina, Alhaji Umar tare da wasu mutum 35 da suka yi garkuwa da su na kwanaki 29 bayan an biya kudin fansa Naira miliyan 26.
’Yan bindigar sun kai hari kauyen ne a ranar 7 ga watan Fabrarirun 2022, inda suka kashe mutum 10 sannan suka sace wasu 36, ciki har da basaraken garin.
- Sabon rikicin kabilanci ya janyo asarar rayuka da kona kasuwa a Abeokuta
- ‘Mutanen da rikicin Ukraine ya raba da muhallansu sun haura miliyan 2’
Kwanaki biyu bayan nan ’yan bindigar sun bukaci a biya Naira miliyan 30 kafin su sake su, abin da ya sa jama’ar kauyen suka dauki lokaci suna ciniki da su domin amincewa da kudin da za su iya biya don fansar ’yan uwansu.
Rahotanni sun bayyana cewa bayan doguwar tattaunawa, ’yan bindigar sun amince su karbi Naira miliyan 10 amma kuma da aka kai musu sai suka ce sun karba ne a matsayin diyyar ’yan uwansu da aka kashe, saboda haka sai an karo miliyan 20.
Abdullahi Umar, wanda da ne ga basaraken, ya ce dole suka koma suka sayar da wasu kadarorinsu suka hada miliyan 16 suka kuma kai a ranar Lahadi, kafin ’yan bindigar su aminta.
Umar ya kara da cewa kowanne mutum da ke garin, ciki har da wadanda ba a dauki ’yan uwansu ba, sun ba da gudummawa wajen tara kudin fansar.
Mun yi kokarun jin ta bakin kakakin ’yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, amma bai dauki waya ko mayar da sakon tes da aka tura mishi ba.