’Yan Bindiga sun sake kai hari kauyen Na’ikko da ke gundumar Kakangi a Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna, inda suka dauke mutane tara.
Har ila yau, wasu maharan sun kuma dauke mutum biyu a kauyen Dala da ke gundumar Kufena a Karamar Hukumar Zariya.
- Kai-Tsaye: Babban Taron Jam’iyyar APC na Kasa
- ’Yan bindiga sun harbe ma’aikacin filin jirgin saman Kaduna
Tagwayen hare-haren na zuwa ne kwana daya bayan maharan sun Kai wani mummunan farmaki a wasu yankuna na Karamar Hukumar ta Giwa ranar Alhamis, inda suka kashe kimanin mutum 50, tare da dauke sama da mutane 100.
Wani ganau a Giwa, Muhammadu Kakangi, ya ce ’yan bindigar sun shiga kauyen Na’ikko ne wajen misalin karfe 11:00 na dare inda suka dauke mutanen; mata biyar da maza hudu.
Ganau din ya ce sunayen mutanen da aka dauken sun hada da Habi Zailani, Samaila Garba, Na’ima Hashimu, Hadiya Sulaiman, Na’ima Ashafa, Zaharaddeen Sulaiman, Salima Rabiu, Dari Jibrin, da kuma Shafarabi Umar.
A wani labarin makamancin wannan, wasu maharan sun dauke mutane biyu a kauyen Dala da ke gundumar Kufena a Karamar hukumar Zariya.
Labarin da Aminiya ta samu, ya nuna cewa maharan sun kai farmakin ne wajen misalin karfe 1:00 na daren Juma’a, inda suka dauke wani miji tare da kanwar matarsa.
Wani kungiyar sa-kai wanda bai son a bayyana sunanshi ya ce mutanen da aka dauka sune Akinjide Odureni, mai kimanin shekara shekara 45 da kanwar matarshi, Mary Odure, mai kimanin shekara 25.
“Maharan tsallaka gidan suka yi, sannan suka dauke mutanen,” inji shi.
Sai dai duk kokarin da Aminiya ta yi na jin ta bakin Kakakin ’Yan Sandar Jihar Kaduna, Mohammed Jalige ta wayar tarho ya ci tura saboda wayar shi ta gagara samuwa har zuwa lokacin hada wannan rahoton.