✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sake sace mutum 3 a Neja

Sun shiga yankin da misalin karfe 12 na dare dauke da bindigogi kirar AK-47.

A wani sabon hari, ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutum uku a yankin Bwari-Sabo da ke Karamar Hukumar Tafa ta Jihar Neja.

Harin na zuwa ne kwana biyu bayan da wasu ’yan bindiga, suka kai farmaki yankin, suka kashe Shugaban Jam’iyyar PDP na Karamar Hukumar, Ishaya Solomon, suka sace matarsa.

Wani mazaunin yankin mai suna Joshua Alfred, ya ce ’yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 12 na daren Alhamis dauke da bindigogi kirar AK-47, inda suka yi garkuwa da mutum uku.

Ya kara da cewa mutanen yankin sun shiga rudani da tashin hankali, yayin harin ’yan bindigar.

Shugaban Karamar Hukumar Tafa, Ibrahim Mami Ijah, ya tabbatar da garkuwa da mutane ukun da aka yi a yankin Bwari-Sabo.

Kakakin ’yan sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, bai amsa kiran wayar wakilinmu ba balantana a ji ta bakinsa.