✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sake sace matar Sarkin Fulani a Abuja

Maharan sun sake sace matar Sarkin Fulanin, bayan sace ta wasu watanni a baya.

’Yan bindiga sun sake sace Habiba Adamu, matar Ardon Fulani da ke Karamar Hukuma Kwali a Abuja, Alhaji Adamu Garba Ardo.

Lamarin ya faru ne da misalin kafe 12: 04 na daren Litinin a Unguwar Tudun Fulani na kauyen ‘Yangoji da ke garin Kwali a Abuja, babban birnin Najeriya.

Khadija Adamu, uwargidan Sarkin Fulanin ce ta tabbtar da faruwar lamarin yayin zantawarta da wakilinmu.

Ta ce ‘yan bindigar sun shiga gidan ne ta baya, inda ta ce da farko sun so tafiya da ita amma sai suka fahimci ba za ta iya tafiya ba saboda tsufa da kuma larurar kafa da take fama da ita.

“’Yan bindigar sun shigo ta karfin tsiya ta wata kofar dakin girki bayan sun kasa bude babban kyauren da ke gaban gidan.

“Dakina suka fara shiga suka tarwatsa komai suna neman kudi,” inji ta.

Ta ce, daga bisani sai ‘yan bindigar suka yi awon gaba da kishiyarta, Habiba Adamu wacce suka taba sacewa a kwanan baya, sannan sun hada da ‘ya ‘yanta 3 – Hafsat da Fatima da kuma Abubakar.

A lokacin da lamarin ya faru, Mai gidansu, Sarkin Fulanin Adamu Garba, ba ya gari.

Bayanai sun ce Sarkin yanzu haka yana garin Idda da ke Jihar Kogi, inda ya kai ziyara domin ganin wasu shanunsa da ke kiwo a can.

Wannan lamari ya faru ne kimanin awa 24 bayan da ‘yan bindigan suka sace wani Mista Sunday Odame Ojarume da matarsa Janet a kauyen Sheda da ke Kwalli.

Wakilinmu da ya tutunbi kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, DSP Adeh Josephine domin samun inganci kan rahoton ba ta ce masa uffan ba.

%d bloggers like this: