Wasu dalibai uku a ranar Talata sun fada tarkon ’yan bindiga a kauyen Gobirawa da ke Karamar Hukumar Safana a Jihar Katsina.
Wani mazaunin kauyen da ya bukaci a sakaya a sunansa ya tabbatar wa da Aminiya faruwar lamarin.
- Kotu ta raba auren shekara 20 kan rashin zaman lafiya
- ‘Yan sanda sun kafa rassa 5 don magance ta’addanci a Sakkwato
- An cafke mutum biyu da bindigogi 27 a Neja
Majiyar ta ce ’yan bindgar sun sace daliban uku ne bayan sun tashi daga wata makarantar sakandiren jeka ka dawo a kauyen na Gobirawa.
“Ba makarantar kwana ba ce, kuma dukkanin daliban uku da aka sace maza ne da aka dauke da tsakar rana yayin da suka kan hanyarsu ta komawa gida bayan an tashi daga makarantar,” a cewar majiyar.
Majiyar ta kara da cewa, ana rade-radin an rufe makarantar bisa umarnin gwamnatin jihar biyo bayan faruwar lamarin.
Sai dai neman tabbatar da ingancin rahoto ya ci tura a yayin da Kwamishinan Ilimin Jihar, Dokta Lawal Badamasi bai amsa kiran wayarsa ba.
Kazalika, jami’in hulda da al’umma na Ma’aikatar Ilimin Jihar, Sani Danjuma ya ce ba ya da masaniya kan faruwar lamarin sakamakon wani uzuri da ya fitar da shi aiki a wajen jihar.
Yayin da aka tuntubi Kakakin ‘yan sandan Jihar SP Gambo Isa domin jin ta bakinsa, ya ce zai tuntubi jami’in dan sanda mai kula da caji ofis na Karamar Hukumar Safana domin samun tabbaci a kan rahoton.