Wasu ’yan bindiga sun kai wa wasu kauyuka hari a yankin Gurmana na Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja yayin da ake kokarin ceto mutum 42 da aka yi garkuwa da su a makarantar gwamnati da ke garin Kagara a Jihar.
Bayan sace dalibai da malaman a Makarantar ta Kagara a cikin tsakar dare, a yamamacin ranar ta Laraba ’yan binidiga suka kai hari a kauyukan Sarkin Zama, Bakin Kogi (Lagbe), Siyiko da masu makwabtaka da su.
- Gimbiyar Dubai: Mahaifina ya yi garkuwa da ni tsawon shekaru
- Yadda ake sayen burodi, haka muke sayen makamai —Daudawa
Majiyarmu ta ce harin da aka yi awanni maharan na ta’asa ya yi sanadin mutuwar mutane da ba a kai ga tantance yawansu ba.
Daya daga cikin shugabannin Kungiyar Matasa Masu Kishin Shiroro, Sani Abubakar Yusuf Kokki ya ce ’yan bindigar sun yi awon gaba da mutane da dama, suka kashe wasu tare da raunata wasu da a halin yanzu suke samun kulawa.
“Hare-haren da ake kawowa babu kakkautawa sun sa yanzu sai yadda ’yan bindiga suka ga dama suke aikatawa.
“An bar mutane da ba su ji ba, ba su gani ba, da ba su da makami su yi ta kansu,” inji shi.