✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sake garkuwa da mutum 9 a Katsina

’Yan bindigar sun fusata ne, inda suka sake garkuwa da wasu a kauyen.

’Yan bindiga sun sake kai farmaki kauyen Albasun Liman Sharehu, da ke Karamar Hukumar Sabuwa a Jihar Katsina, inda suka yi garkuwa da mutum tara.

Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne da sanyin safiyar ranar Laraba.

Wakilinmu ya ruwaito cewa daga cikin wadanda aka yi garkuwar da su, har da dalibin aji biyu na Babbar Sakandire ta Damari da kuma mahaifinsa.

Idan ba a manta ba, ko a ranar Kirsimeti sai da ’yan bindigar suka kai farmaki kauyen, inda suka yi garkuwa da mutum takwas ciki har da matan aure biyu.

Sai dai mutum takwas din da aka yi garkuwa da su a satin da ya gabata sun tsere yayin da ’yan bindigar ke barci.

A cewar wata majiya daga kauyen, ’yan bindigar sun fusata ne suka sake dawowa sakamakon tserewar mutanen.