✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace ’yan sanda 12 a hanyar Zamfara-Katsina

Mahara sun sace ’yan sanda 12 da ke aiki a Jihar Borno a hanyar Katsina zuwa Zamfara.

’Yan bindiga sun sace jami’an ’yan sanda 12 da ke aiki da rundunar a Jihar Borno a kan hanyar Katsina zuwa Zamfara.

Wata majiya daga jami’an tsaro ta shaida wa sashen Hausa na BBC cewa an sace ’yan sandan ne, yawancinsu masu mukamin ASP a kan hanyarsu ta zuwa wasu jihohin Arewa maso Yamma domin gudanar da aiki lokacin da lamarin ya faru.

Majiyar ta ce jami’an sun yi batar dabo ne kafin su kai ga inda suka dosa, kuma ko da daya daga cikinsu bai samu ya tsira daga maharan ba.

Matar daya daga cikin ’yan sandan da aka kama wacce ta yi magana da ’yan jarida ta ce mijin nata ya kira waya yana umartarta da a sayar da gidansa domin a hada Naira miliyan dayan da zai biya su a matsayin kudin fansa.

Ta ce, “Mijina ya kira ni a ranar Laraba da misalin karfe 8:00 na dare yake shaida min abin da ya faru.

“Ya umarce ni da na sayar da gidan domin mu samu kudin fansa. Ya ce min rayuwarsa na cikin hadari muddin ba mu kawo kudin ba, daga nan ya katse wayar. Har yanzu ba mu hada kudin ba.

“Daga bisani kuma wani daga cikin wadanda aka sace din shi ma ya kira ni ya ce min an ce kowannensu sai ya biya N800,000.

“Tun daga lokacin muka shiga halin dimuwa, ba ma mu san makomar mu ba. Mun dogara ga Allah kawai ya kawo mana mafita.

“Muna kira ga Gwamnatin Najeriya da ta taimaka ta shiga lamarin”, inji ta.

Sai dai da aka tuntubi Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Borno ta ce za ta nemi karin bayani daga wurin da aka yi ittifaki a nan ne lamarin ya faru.

Su kuwa masu magana da yawun rundunar a jihohin Zamfara da Katsina sun ce ba su da masaniya a kan lamarin.