✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace wata mata mai ’ya’ya uku

Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wata mata mai ’ya’ya uku, Tina Etameta, a shagonta. Majiyarmu ta ce…

Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wata mata mai ’ya’ya uku, Tina Etameta, a shagonta.

Majiyarmu ta ce an sace Etameta, mai shekara 44 ne a shagonta na sayar da kayan abinci a Karamar Hukumar Ughelli ta Jihar Delta.

Ta ce masu garkuwar sun yi ta harbi a iska bayan isarsu wurin kafin su tafi da ita zuwa inda ba a sani ba.

Mijinta, Mista Lucky Etemata, wanda abin ya faru a gabansa, ya ce ya tsere ne a lokacin da maharan ke ta harbe-harbe.

Ya kara da cewa daga baya ’yan bindigar suka yi awon gaba da matar tasa, wacce ta gudu zuwa cikin shago domin ta boye.

Kokarin jin ta bakin kakakin Rundunar ’Yayan Sanda DSP Onome Onovwakpoyeya bai yi nasara ba, amma wani babban jami’in rundunar a yankin Ughelli ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce ’yan sanda na kokarin kubutar da matar daga hannun ’yan bindigar.