✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace wasu mata a kantin magani

Maharan sun yi awon gaba da waat mata da ta kai danta domin a duba lafiyarsa

’Yan bindiga sun sace wasu mata biyu a wani kantin magani ranar Talata a Fatakwal, Jihar Ribas.

Majiyarmu ta ce, matan da aka sace sun hada da wata ma’aikaciyar kantin maganin da wata wata da ta kai danta shagon don a duba shi sakamakon rashin lafiya.

Wani ganau ya ce, “Da alama ’yan bindigar sun bi sawun matar da ta kai danta mara lafiya kantin ne.

“Saboda tana sauka daga mota, barayin suka fito suka damke ta tare da ma’aikaciyar kantin sannan suka kara gaba,” in ji shi.

Tuni dai aka sanar da ’yan sandan yankin abin da ya faru domin su yi aikinsu.

Garkuwa da mutane, wanda gwamnatin Najeriya at ayyana a matsayin  laifin ta’addanci, na daga cikin manyan kalubalen da suka addabi kasar duk kuwa da kokarin gwamnati da jami’an tsaro wajen yakar matsalar.