Wasu ’yan bindiga a Jihar Akwa Ibom sun sace tsohon Sanatan da ya wakilci Kudancin Jihar a Majalisar Dattijai ta takwas, Sanata Nelson Effiong.
Rahotanni sun ce wasu ’yan bindiga su uku ne suka yi awon gaba da dan siyasar wanda kuma tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar ne daga wani fitaccen sahgo da ke kan titin Oron na birnin Uyo da daren Lahadi.
Maharan sun kuma jikkata wasu mutum takwas, ciki har da wadanda aka harba yayin yunkurin sace tsohon Sanatan.
Daya daga cikin wadanda suka ji rauni mai suna Ekwere Ekwere ya ce ya ankarar da wasu ’yan jarida ne ta wani dandalin WhatsApp kan harin, inda ya ce shi ma da kyar ya sha.
Kazalika, wata majiyar da ta bukaci a sakaya sunanta ta ce an yi awon gaba da tsaohon Sanatan ne a cikin wata mota kirar Toyota Camry zuwa wani waje da ba a san ko ina ne ba.
“Lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na daren ranar Lahadi. Mutanen dauke da makamai a kan motarsu kirar Toyota Camry sun yi wa ginin kawanya sannan suka fara harbin kan mai uwa da wabi kafin suka tarwatsa jama’a sannan su dauke shi,” inji majiyar.
Kakakin ’yan sandan Jihar, SP Odiko Macdon ya tabbatar da faruwar harin inda ya ce suna nan suna bincike a kai.
“Na yi imanin nan ba da jimawa ba, za mu ceto shi. Kwamishinan ’yan sanda ya kuma yi Allah-wadai da harin kuma ba za a yi wata-wata ba wajen ceto shi,” inji Kakakin ’yan sandan.