✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace shugaban Kwaleji a Zamfara

An sace shi ne a gidansa da ke Bakura da sanyin safiyar ranar Lahadi.

’Yan bindiga a Jihar Zamfara sun sace shugaban Kwalejin Fasaha da Kimiyyar Dabbobi ta Jihar, Habibu Mainasara.

An dai sace shi ne daga gidansa da ke garin Bakura da sanyin safiyar ranar Lahadi.

Har yanzu dai babu cikakkaun bayanai kan lamarin.

Hakan na zuwa ne ’yan sa’o’i kadan bayan ’yan bindigar sun hallaka kimanin manoma 40 a wansu jerin hare-hare da suka kai kauyuka biyar da ke Jihar.

Sassa da dama na Najeriya dai sun jima suna fuskantar matsalar tsaro kuma dukkan wani yunkuri na magance matsalar na neman ya gagari Kundila.

Harin da kuma na zuwa ne ’yan sa’o’i bayan wasu ’yan bindigar sun kai hari Fadar Sarkin Kajuru a Jihar Kaduna tare da tafiya da sarkin da kuma wasu iyalansa 12.