✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace sarki da iyalansa 12 a Kaduna

’Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da iyalan basaraken guda 12.

Wasu ’yan bindiga sun sace Sarkin Kajuru mai daraja ta biyu, Alhaji Alhassan Adamu a gidansa da ke Kajuru a Jihar Kaduna.

’Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da iyalan basaraken guda 12, ciki har da mata da kananan yara.

Jikan basaraken, kuma mai rike da sarautar Dan Kajuru a masarautar, Sa’idu Musa ne ya tabbatar da hakan ga Aminiya.

Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:30 na daren ranar Asabar.

Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, da kakakin ’yan sandan Kaduna, Mohammed Jalige basu amsa kiran wayar da aka yi musu a kan lamarin ba.

Wannan dai shine hari na baya bayan nan daga cikin irin hare-haren da ake kai wa a Jihar ta Kaduna.

Ko da yake ’yan bindigar sun jima suna cin karensu ba babbaka a Jihar, amma a ’yan kwanakin nan abubuwa sun dada ta’azzara.