✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace mutum 87 a wani sabon hari a Kaduna

Har kawo yanzu babu amo ballantana labarin wadanda ’yan bindigar suka sace.

Akalla mutum 87 aka yi garkuwa da su yayin wani sabon hari da ’yan bindiga suka kai kauyukan Gangere da Aguna da ke karkashin gundumar Kufana ta Karamar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna.

Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin.

Duk da cewa babu wasu cikakkun bayanai game da faruwar lamarin, sai dai har kawo yanzu babu amo ballantana labarin wadanda lamarin ya rutsa da su.

Wani mazauni kuma shugaban matasa, Ben Yuhana, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, “’yan bindiga sun shiga kauyukan Gangere da Aguba da ke gundumar Kufana ta Karamar Hukumar Kajuru inda suka yi garkuwa da mutane 87 a tsakanin daren jiya zuwa safiyar yau.

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar hukumance, a yayin da Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida bai mayar da martani kan sakon kar ta kwana da Aminiya ta aika masa ba.

Sai dai mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan wanda Aminiya ta tuntuba, ya ce zai yi karin haske da zarar ya samu cikakkun bayanai gama da faruwar lamarin.