Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace mutum shida a yankin Tungan-Maje da ke Gwagwalada a Abuja, babban birnin Najeriya.
Wani mazaunin yankin mai suna Yahaya, ya bayyana cewar lamarin ya faru da misalin karfe 11:46 na daren ranar Litinin, yayin da ’yan bindigar suka farmaki Unguwar Dabiri da Unguwar Sarki a yankin.
- An yi garkuwa da mahaifiyar Sakataren Gwamnatin Bayelsa
- Abale: Nas din da ya yi fice da dabanci a Kannywood
Ya ce ’yan bindigar sun kasu gida uku inda suka kai farmaki gidaje uku sannan suka yi awon gaba da mutane.
“Wasu daga ’yan bindigar sun tsaya a waje yayin da ragowar suka cikin gidajen suka yi awon gaba da mutane sannan suka tsere cikin daji da su,” inji Yahaya.
Mai garin Tungan-Maje, Alhaji Hussaini Barde ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma koka kan yadda ’yan bindiga suka addabi garin.
“Ayyukan ’yan bindiga a Tungan-Maje ya dade yana barazana ga zaman lafiyar jama’ata.
“Ina mai tabbatar da cewar tun daga Satumbar bara ’yan bindiga sun kawo munanan hare-hare guda 9,” a cewarsa.
Tungan-Maje, ya nemi masu ruwa da tsaki da su kawo wa yankin nasu dauki duba da yadda ake musu dauki dai-dai.
Sai dai neman jin ta bakin kakakin ’yan sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf ya ci tura, a yayin da ba ta amsa kiran wayarta ba ko mayar da sakon kar-ta-kwana da wakilinmu ya aike mata ba.