’Yan bindiga sun afka wa kauyen Katsalle da ke Karamar Hukumar Sabuwa a Jihar Katsina inda suka yi garkuwa da mutum 30, wadanda yawacinsu mata ne.
Wani mazaunin Katsalle ya shaida wa Aminiya a waya cewa ’yan bindiga kusan 40 ne suka auka wa kauyen a kan babura da misalin karfe 12 na ranar Litinin.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum uku a Kaduna
- An yanke wa ’yan Najeriya biyu hukuncin kisa a Ghana
- An kusa ci gaba da haska shirin Labarina —Aminu Saira
“Da muka ga sun shigo, sai muka buya.
“Mun yi kokarin kai wa mata dauki amma abin ya gagara, saboda muna jin kukan kananan yaran na neman taimako; babu yadda za mu yi.
“Akwai wani gida da suka dauki mata 10,” inji shi.
A ranar Lahadin da ta gabata, rahotanni sun ce ’yan bindiga sun kai hari kauyukan Unguwar Tukur da Sabon Layin Mai Keke, inda a Unguwar Tukur suka sace mata 10, sannan aka dauke mutum 15 a Sabon Layin Mai Keke.
Kokarinmu na jin ta bakin kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar Katsina, SP Gambo Isa, bai yi nasara ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Amma Sashen Hausa na BBC ya nakalto yana cewa suna jiran rahoton daga Jami’in ’Yan sanda na Shiyyar.