✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace mutum 37 a kwana 3 a Kaduna

Galibin wadanda aka sacen mata ne, ciki har da masu shayarwa da kananan yara.

Akalla mutum 37 ’yan bindiga suka sace a hare-haren da suka kai wasu kauyukan Jihar Kaduna a cikin kwana ukun da suka gabata.

Kauyukan da lamarin ya shafa sun hada da Azara da Janjala da kuma Kadara, cikin kananan hukumomin Kagarko da Kachia a jihar.

Aminiya ta gano galibin wadanda lamarin ya shafa mata ne, ciki har da masu shayarwa da kuma kananan yara.

Yayin hare-haren, ’yan bindigar sun kashe wani tsohon soja da dansa a kauyen Katambi da ke makwabtala da garin Kateri.

Da yake tabbatar wa Aminiya da aukuwar lamarin a ranar Alhamis, Sarkin Azara, Mustapha Ibrahim, ya ce maharan sun shiga garin ne da tsakar dare dauke da bindigogi suka kwashi mutum 10 ciki har da mata masu shayarwa.

Ya ce kafin su kai ga sanar da sojojin da ke sintiri a yankin abin da ke faruwa, ’yan ta’addar sun riga sun tsere.

Rugar Alhaji Karbo da kauyen Kurutu da wani kauyen Kadara da Janjala a Kagarko da sauransu, na daga yankunan da hare-haren ta’addancin suka hana wa barci ido rufe in ji majiyarmu.