Kimanin mutum 18 ’yan bindiga suka sace tare da kashe mutum guda a Unguwar Zalla da ke yankin Udawa a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 12.30 na daren Asabar wayewar garin Lahadi a garin da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.
- Gobara ta tashi a matatar mai ta Fatakwal
- 2023: Zan rushe duk tabargazar El-Rufa’i in na zama Gwamnan Kaduna – Shehu Sani
Wani jagoran al’umma a yankin da ya tabbatar da faruwar lamarin, Muhammad Umar, ya ce wani mai suna Bala Jaja shi ne mutumin da ’yan bindigar suka kashe.
Kazalika, ya bayyana cewa cikin wadanda ’yan bindigar suka yi awon gaba da su har da matan aure da ’yan mata.
Sai dai har kawo yanzu hukumomi ba su ce uffan a kan lamarin ba, kuma neman jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige ya ci tura.
Jihar Kaduna na daga cikin jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya da hare-haren ’yan bindiga suka tsananta wadanda suke satar mutane da neman kudin fansa da kuma kashe su a wasu lokutan.