✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace mutum 12 a Kaduna

’Yan bindiga sun sace aƙalla mutum 12 cikin wasu jerin hare-hare mabanbanta da suka kai ƙauyukan Libere da Unguwar Babangida da ke Karamar Hukumar Kauru…

Yan bindiga sun sace aƙalla mutum 12 cikin wasu jerin hare-hare mabanbanta da suka kai ƙauyukan Libere da Unguwar Babangida da ke Karamar Hukumar Kauru a Jihar Kaduna.

Wani Shugaban Matasa a yankin, Aminu Khalid, ya bayyana cewa cikin waɗanda ’yan bindigar suka yi awon gaba da su har da wasu ma’aurata da suka fita aikin gona a ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa washegari Juma’a ce ’yan ta’addan suka kai hari Unguwar Babangida inda suka ce mai unguwar, Malam Babangida Sogiji da wasu ƙarin mutum shida.

Ya ƙara da cewa, biyu daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su manoma ne daga Jihar Jigawa da ke zuwa shekara-shekara domin aikin gona.

“Sai dai kawo yanzu waɗanda suka sace mutanen ba su tuntubi kowa ba game da biyan kuɗin fansa, inji shi.

Khalid ya bayyana matuƙar damuwa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a yankin a dalilin ayyukan masu yi wa ’yan ta’adda leƙen asiri.

Matashin ya kuma bayyana cewa Libere na ɗaya daga cikin ƙauyukan da ’yan bindiga suke mamaya a bayan nan, inda yake kira ga jami’an tsaro da suka musu ɗauki.

Ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kaduna, Mansir Hassan ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.