✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace mutane da dama a kauyen Zamfara

Wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun afka wa kauyen Nahuche na Karamar Hukumar a Jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba…

Wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun afka wa kauyen Nahuche na Karamar Hukumar a Jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da wasu mazauna garin ciki har da mata da kananan yara.

Mazauna kauyen sun shaida wakilinmu cewa, mutanen dauke da makamai sun afka wa kauyen a ranar Alhamis inda suka fara harbe-harbe a iska.

“Dukkanmu mun firgita a yayin aukuwar wannan musiba inda kowanenmu ya ranta a na kare wajen neman mafaka.”

“Mutanen sun kawo harin ne a kan Babura amma suka ajiye su a bayan gari gabanin su shigo kauyen.”

“Ba za mu iya fadin takaimaman adadin mutanen da suka sace ba a yanzu, amma wasu daga cikin matanmu na daga cikin wadanda abin ya ritsa da su kuma tuni muka ankarar da jami’an tsaro domin su kawo mana dauki,” cewar wani mazaunin kauyen.

Kazalika, gwamna Muhammad Bello Matawalle, ya sanar da samun rahoton wannan hari a wani sakon kar ta kwana da ya ce an aike masa yayin wani taro da ya yi tare da masu ruwa a Gusau, babban birnin Jihar.