’Yan bindiga sun kai hari tare da sace akalla mutum 36 a unguwar Keke B da ke Kaduna.
Maharan sun far wa unguwar ce da misalin karfe tara na dare ranar Litinin suka yi ta shiga gidaje suna tisa keyar mutane zuwa cikin daji.
- ’Yan ta’adda sun kashe sojojin Rundunar Tsaron Shugaban Kasa a Abuja
- Yadda mata masu kiba ke fama da masu kushe halittarsu
Wani ganau, Muhammad Salihu, ya ce, “’Yan bindigar sun rika harbi a iska suna shiga gida-gida suna tafiya da mutane.
“Wani mai gyaran babur ya samu ya tsere daga hannunsu amma sun tafi da mutum 36,” inji Muhammad.
An tafi da surukata
Wani mazaunin unguwar Keke A, da aka sace surukarsa a harin na Keke B, ya shaida wa Aminiya cewa, “Sun tafi da ’yar uwar mahaifiyar matata da ’yarta budurwa da wani danta.
“Kafin su tafi, sun bar mijinta suka sa wani daga cikinsu ya harbe shi; har ya sa bindiga a kansa zai harbe shi, sai ya fasa, suka wuce da su ba su ce mishi komai ba.”
Ya ce, “Daga baya can cikin dare sai ga dan nata ya dawo; ya ce bayan ’yan bindigar sun tafi da su ne ya fita a guje ya yi cikin daji, amma ba su kama shi ba.
“Yanzu haka mutane sai shirin fita ake ta yi daga unguwar; ka san nan unguwar (Keke A) duk abin da ya faru a dan zagayen nan sai a yi ta guduwa.
An sace ma’aurata da dansu na goye
Wata Malama Salamatu, wadda yayarta ke zaune a Keke B ta ce, ’yar uwar tata ta ce, “Gida biyu ne kawai a layinsu ’yan bindigar ba su shiga ba — kuma sun tafi da mutane da yawa.
“Sun shiga gidansu makwabciyar yayar tawa suka tafi da iyayenta da kaninta na goye da yayarta; kananan yaran gidan kawai suka bari, su ma a gidan yayyensu suka je suka kwana.
“Akwai wani direba ma da kwanaki aka sace, to yanzu ma sun tafi da iyalansa.”
Ta ce mutanen sun bar unguwar ne da misalin karfe 10 na dare.
“Sai daga baya mutanen unguwar ke ta fada wa juna an tafi da wane, wane ma sun tafi da shi,” inji ta.
Kawo yanzu dai babu wani cikakken bayani game da adadin mutanen da harin ya ritsa da su ko wata sanarwa daga hukumomin tsaro kan lamarin.
Akalla karo na biyu ke nan da ’yan bindiga ke kai hari a yankin Keke da ke Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Ko kafin Babbar Sallah sun kai hari a Unguwar Keke A, suka sace mutane.
Yankin Dambushiya da Kadaure da ke yankin Sabuwar Kaduna ma ba su tsira daga irin wadannan hare-hare ba.